IS ta kaddamar da hari a birnin Kirkuk na Iraqi

Gwamnan Kirkuk ya ce yanzu kura ta lafa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Gwamnan Kirkuk ya ce yanzu kura ta lafa

'Yan kungiyar IS sun kai hare-hare a gine-ginen gwamnati da ke birnin Kirkuk na kasar Iraqi da kewayensa.

Kafofin watsa labarai na kasar sun rawaito cewa wasu 'yan kunar-bakin-wake sun kai hare-hare a ofisoshin 'yan sanda da na ma'aikatar samar da wutar lantarki, kodayake jami'an tsaro sun kore su.

Wani kamfanin dillacin labarai da ke da alaka da kungiyar ta IS ya yi ikirarin cewa mayakan kungiyar sun kutsa kai cikin babban dakin taro na Kirkuk sannan sun kwace babban otal din birnin.

Mayakan na IS sun kai hare-haren ne a daidai lokacin da dakarun gwamnatin Iraqi ke kokarin sake kwace birnin Mosul wanda ke arewacin kasar.

Rahotanni na cewa mayakan IS sun banka wuta a wata tashar sinadarai da ke kudancin Mosul kafin su janye daga birnin ranar Alhamis.