Za'a rage yin giya a duniya

Daya daga cikin kamfanonin da ake yin giya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Daya daga cikin kamfanonin da ake yin giya

Ana saran adadin giyar da ake yi duniya zai ragu sakamakon mummunar yanayi.

Wata kungiya ta kasa da kasa ta masu yin giya ta ce raguwar za ta fi shafar kasashen da suka hada da Brazil da Argentina da Chile da kuma kasar Faransa.

An dai sa ran raguwar giyar da ake samarwa a Faransa ne bayan da fari ya abkawa gonakin alkamar da ake yin giya da ita.

Sai dai kungiyar ta ce za'a samu karuwar giyar da ake samarwa a wasu kasashe kamar Spaniya da Amurka.

Kungiyar ta daura alhakin bambancin alkaluma na yawan giyar da ake yi kan abin da ta kira al'amuran da suka shafi yanayi.