Nigeria ta yi sama zuwa mataki na 11 a Afirka

Asalin hoton, The NFF
Super Eagles ba za ta buga gasar kofin Afirka da za a yi a 2017
Nigeria ta matsa sama zuwa mataki na 11 a jerin kasashen da suke kan gaba a iya taka leda a Afirka a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fifa, ta fitar a ranar Alhamis.
Haka kuma Nigeria tana matsayi na 60 a jerin tawagogin kwallon kafa da suka yi fice a fagen tamaula a duniya.
A jadawalin baya da Fifa ta fitar a cikin watan Satumba, Nigeria ce ta 14 a iya kwallon kafa a Afirka ta 64 a fagen tamaula a duniya.
Cote d'Ivoire ce ta daya a iya taka-leda a Afirka, sai Senegal a matsayi na biyu, inda Algeria ce ta uku.
A duniya kuwa Argentina ce ta daya sai Jamus mai rike da kofin duniya a mataki na biyu, inda Brazil ke matsayi na uku.