Aisha Muhammad: Na yi mamakin lashe gasar Hikayata

Aisha Muhammad: Na yi mamakin lashe gasar Hikayata

Gidan rediyon BBC Hausa ya bayyana Aisha Muhammad Sabitu a matsayin macen da ta lashe gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai.

Aisha, wacce ta fito daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, ta rubuta kagaggen labarinta ne mai suna "Sansanin 'Yan Gudun Hijira".

Labarin nata ya yi tsokaci ne kan mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suka samu kansu a wani sansani da ke jihar Adamawa.

Ta yi bayani kan yadda ta ji da wannan nasara da ta samu, inda har ta zubar da hawaye.