Ana hana fararen hula ficewa daga Aleppo-Sergei Lavrov

Asalin hoton, Reuters
Rikicin Syria ya sanya fararen hula da dama cikin mawuyacin yanayi
Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya zargi kungiyoyin 'yan tawayen Syria da hana fararen hula barin wuraren da aka yi wa kawanya a birnin Aleppo.
Mr Lavrov ya yi wannan zargi ne a lokacin da ya ke magana ta wayar tarho da takwaransa na Amurka John Kerry, sa'oi kadan bayan yarjejeniyar tsagaita wuta saboda ayyukan jin kai da Rasha ta ayyana ta fara aiki.
Yarjejeniyar tsagaita wutar za ta bawa mayakan 'yan tawayen da fararen hula damar wucewa ko ta bangaren da gwamnati ke iko da shi a yammacin Aleppo ko kuma ta bangaren da 'yan tawayen ke da karfi a Idlib.
'Yan tawayen dai sun yi watsi da tayin da Rasha ta yi.Majalisar dinkin duniya ta ce ta na fatan za a fara kwashe wadanda suka samu munanan raunuka a Aleppo daga ranar Jumma'a.