Afrika ta Kudu za ta fice daga kotun Duniya ta ICC

Gini kotun ICC
Bayanan hoto,

Kotun ta ICC dai na neman shugaba Bashir saboda zargin da ake masa na aikata laifukan yaki.

Gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya cewa za ta janye wakilcinta daga Kotun Hukunta Manya Laifukka ta Kasa-da-kasa wato ICC.

Kasar ta sanar da shirinta na daukar matakin ne a cikin wata wasika da ta aike wa majalisar ta hannun jami'an diplomasiyyarta.

Kasashe da dama ne ke zargin kotun ta ICC da mayar da karfinta kan nahiyar Afrika tana kau da kai daga abubuwan ake tafkawa a sauran kasashen duniya.

Matakin janyewar ya fito fili da irin halin tsaka-mai-wuyar da kasar ta Afrika ta kudu ta fuskanta a bara a lokacin da aka hura mata wuta a kan sai ta kama shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a yayin wani taron kungiyar Tarayyar Afrika a birnin Johannesburg.

Wannan matakin dai na zuwa ne mako daya bayan da shugaban kasar ta Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ziyarci kasar Kenya, wata kasa da ke matukar sukar kotun ta ICC kan gurfanar da shugabanta Uhuru Kenyatta.