Aguero da Kompany za su ci gaba da zama a City —Guardiola

Guardiola ya ce ba shi da niyayyar korar 'yan wasan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Guardiola ya ce ba shi da niyayyar korar 'yan wasan

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya yi watsi da labaran da ke cewa yana yunkurin korar Sergio Aguero da Vincent Kompany daga kulob din.

'Yan wasan biyu dai ba su shiga wasan da City ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 4-0 a gasar cin kofin zakarun turai ranar Laraba ba, inda Kompany bai shiga jerin ko da 'yan wasan da ke benci ba.

Hakan dai ya sa ana ta rade-radin cewa ba sa cikin 'yan wasan da Guardiola zai rika damawa da su.

Sai dai kocin ya ce "Ba zan kore su ba. Suna da makoma a wannan kungiyar. Vincent ba shi da koshin lafiya shi ya sa ban sanya shi a wasan ba. Ban kuma sanya Sergio ba ne kawai saboda ina da wani tsari a kansa."

Guardiola ya shaida wa manema labarai cewa ya kamata su tuntube shi kafin su rubuta labarin cewa yana son korar Aguero, yana mai cewa: "Idan Sergio ya yanke shawarar barin kungiyar, to lallai hakan shi ta shafa."

Guardiola ya tabbatar cewa Pablo Zabaleta da Bacary Sagna ba za su buga wasan da za su yi da Southampton a Etihad na cin kofin Premier ranar Lahadi ba saboda rashin lafiya.