Hadarin jirgin kasa ya hallaka mutum 55 a Kamaru

Jirgin na dauke da mutane fiye da kima

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jirgin na dauke da mutane fiye da kima

Hukumomin kasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane 55 a wani mummunan hadari jirgin kasa da ya faru ranar Juma'a.

Haka ma sun ce wasu kusan 600 sun samu raunukka a cikin hadarin wanda ya faru lokacin da jirgin ya kauce hanya a yankin Eseka wanda ke tsakanin manya biranen kasar biyu - Douala da Yaounde.

Jirgin dai na kan hanyarsa ne ta zuwa birnin Douala daga babban birnin kasar wato Yaounde.

Kawo yanzu dai ba tabbatar da sanadin hadarin ba amma wakilinmu a kasar ta Kamaru ya ce an kiyasta cewa kimanin taragai 11 ne suka jirkice bayan da jirgin ya kauce hanya.