Ana ci gaba da gwabza fada a birnin a Mosul

Mosul, Iraq

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Su ma sojan Kurdawa da ke gabashin birnin na fuskantar barin wuta a kusa da Ba'ashiqah.

Fafatawar da ake yi domin fatattakar 'yan kungiyar IS daga birnin Mosul da ke arewacin Iraki ya shiga rana ta shida inda sojojin Iraqin ke cewa suna samun tirjiya sosai.

Wani wakilin BBC wanda ke tafiya tare da sojojin Irakin ya ce mayakan na mayar da martani ne da hare-haren kunar bakin wake ta hanyar tuko motoci makare da makamai da gudu suna tunkarar inda sojojin suka ja daga.

Sai dai su kuma sojojin na Iraqi na harba musu makamai masu linzami.

Ana fargabar cewa fararen hula fiye da miliyan guda ne ke makale a cikin birnin na Mosul, kuma akwai yiwuwar za a samu kaurar jama'a mai dimbin yawa idan fadan ya kai tsakiyar birnin.