Jirgin Rasha ya fadi a arewa maso yammacin Siberia.

Mutane 19 ne suka mutu a cikin jirgin
Bayanan hoto,

Mutane 19 ne suka mutu a cikin jirgin

Mahukunta a Rasha sun ce akalla mutane 19 sun mutu a wani hadarin jirgi mai saukar ungulu da ya afku a arewa maso yammacin Siberia.

Mai magana da yawun ma'aikatar agajin gaggawa na kasar ya ce tuni aka fara aikin nema da kuma ceto a wajen da abin ya faru.

An dai yi amanna cewa mutane uku sun tsira da ransu.

Mahukuntan sun ce yanayin wajen da abin faru sam ba shi da kyau sosai.