Neymar ya sabunta kwantaraginsa a Barcelona

Asalin hoton, Rex Features
Neymar ya ci kwallaye shida a wasanni tara da ya buga wa Barca a kakar wasa ta bana
Dan wasan gaba na Barcelona Neymar ya sanya hannu a sabon kwantaragin shekara biyar da kungiyar, wata uku bayan ya amince ya ci gaba da murza mata leda.
Yanzu dai Neymar zai ci gaba da zama a kungiyar akalla zuwa shekarar 2021.
Dan wasan mai shekara 24 zai rika karbar £178m daga ranar daya ga watan Yuli.
Kazalika zai karbi £200m a shekara ta biyu da sanya hannu a kan kwantaragin, yayin da zai rika karbar yuro 250m a shekaru uku na karshe.
Neymar ya zura kwallaye 91 a wasanni 150 da ya buga wa kungiyar tun da ta saye shi a shekarar 2013.
Kocin Barca Luis Enrique ya ce,"Sabunta kwantaragin da Neymar ya yi babban labari ne. Ya nuna yadda yake ci gaba a Barca da kuma yanayin taka ledarsa da ya sa ya zama daya daga cikin gwarazan 'yan wasa a duniya."
Neymar ya dauki kofunan La Liga biyu da na zakarun turai guda daya da kuma na Copa del Rey guda biyu a kungiayr ta Barca.