Trump ya caccaki Michelle Obama

Trump ya ce Michelle Obama bata iya komai ba sai yakin neman zabe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Trump ya ce Michelle Obama bata iya komai ba sai yakin neman zabe

Dan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya caccaki mai dakin shugaban kasar Michelle Obama, yana mai cewa babu abin da ta iya "sai yi wa abokiyar hammayata yakin neman zabe."

Ya kuma zarge ta da sukar Hillary Clinton a shekarar 2007 lokacin da ita da Barack Obama ke neman jam'iyyar Democrat ta tsayar da su takarar shugaban kasar.

Sai dai ofishin yakin neman zaben Obama ya musanta cewa Michelle Obama ta soki Mrs Clinton.

A nata bangare, Mrs Clinton ta soki Mr Trump, tana mai cewa yana yin barazana ga dimokradiyyar kasar saboda kin cewa zai amince da sakamakon zabe idan ya sha kaye.

Ta shaida wa wani taron yakin neman zabenta a birnin Cleveland na jihar Ohio cewa, "mun san bambancin da ke tsakanin shugaba na kwarai da dan kama-karya. Mika mulki cikin kwanciyar hankali shi ne bambancinsu. Donald Trump ya ki cewa zai amince da sakamakon zaben idan bai yi nasara ba. Idan kuwa haka ne, lallai yana barazana ga dimokradiyyar kasar nan."