Hadarin jirgin kasa ya hallaka mutum 70 a Kamaru

Jirgin na dauke da mutane fiye da kima

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jirgin na dauke da mutane fiye da kima

Shugaban Kamaru Paul Biya ya tabbatar da mutuwar mutum 70 a mummunan hadarin jirgin kasar da ya faru a kasar ranar Juma'a.

Paul Biya ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Shugaban kasar ya kara da cewa mutum 600 sun samu raunuka a hadarin wanda ya faru lokacin da jirgin ya kaucedaga kan layinsa a yankin Eseka wanda ke tsakanin manyan biranen kasar biyu - Douala da Yaounde.

Mr Biya ya ce, ''Na bai wa jami'an gwamnati umarnin bayar da taimako ga mutanen da suka tsira daga hadarin jirgin, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin hadarin jirgin.''

Jirgin dai na kan hanyarsa ne ta zuwa birnin Douala daga babban birnin kasar wato Yaounde.

Wakilinmu a kasar ta Kamaru ya ce an kiyasta cewa kimanin taragai 11 ne suka jirkice bayan da jirgin ya kauce daga kan layinsa.