Andres Iniesta zai yi jinyar mako takwas

Asalin hoton, EPA
Ivan Rakitic ya maye gurbin Iniesta bayan ya ji rauni
Kyaftin din Barcelona Andres Iniesta zai yi jinyar mako shida zuwa takwas sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa a wasan da suka doke Valencia.
Dan wasan na tsakiya ya ji rauni ne a lokacin da suka yi taho-mu-gama da Enzo Perez a minti 14 da soma wasan da aka tashi da ci 3-2, ida aka dauke shi a gadon daukar marasa lafiya.
Mai yiwuwa ba zai buga sauran wasannin da za a yi na gasar cin kofin zakarun turai ba, kuma ba zai buga karawar da za su yi da Manchester City ranar daya ga watan Nuwamba ba.
Barca ta yi nasara a wasan ne sakamon kwallon da Lionel Messi ya ci bayan sun samu bugun fenareti.
Haka kuma 'yan wasan Barca biyu -- Gerard Pique da Jordi Alba -- ba za su buga wasan da kungiyar za ta yi da City ba saboda raunin da suka ji.