AT&T zai sayi Time Warner a kan $86bn

Wannan ciniki na daya daga cikin mafiya girma a bana

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wannan ciniki na daya daga cikin mafiya girma a bana

Katafaren kamfanin samar da layukan wayar salula na Amurka AT&T ya ce zai sayi kamfanin fina-finai Time Warner a kan kimanin $86bn.

Wannan ciniki shi ne daya daga cikin mafi girma da aka yi a wannan shekarar, kodayake sai sun samu amincewar hukumomin da ke sanya ido a fannin sadarwa.

Idan komai ya tafi kamar yadda aka tsara, za a hada tasoshin rarraba labarai na AT&T da rukunin dakunan shirya fina-finai na Warner Brothers da kuma tasoshin talabijin na tauraron dan adam na HBO da CNN.

Shugaban AT&T ya bayyana cinikin a matsayin "wanda ya dace" amma masu suka sun ce lamarin ya bai wa kafofin watsa labarai karfi.

Hukumomin da ke sa ido kan kafafen watsa labarai na Amurka dai za su sa ido sosai kan wannan ciniki.

AT&T dai ita ce tashar talabijin din tauraron dan adam ta uku mafi girma a Amurka.

Sai dai shugaban AT&T Randall Stephenson ya ce ba ya tsammanin samun wata matsala daga wajen masu sanya idanun, yana mai cewa komai zai yi daidai.