Mayakan IS sun kai sabon farmaki a Iraqi

Mutanen da dama sun tsere daga Mosul da kewayensa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mutanen da dama sun tsere daga Mosul da kewayensa

Mayakan kungiyar IS sun kaddamar da hare-hare a wani kauye da ke lardin Anbar na kasar Iraqi a kokarin da suke yi na kawar da hankalin dakarun gwamnati daga kwace birnin Mosul daga hannunsu.

Magajin garin Rutba ya bayyana hare-haren da mayakan na IS suka kai garin nasa ta bangarori uku da cewa suna da "matukar tsoratarwa."

Imad Meshaal ya ce an yi arngama tsakanin mayakan IS da dakarun tsaro a tsakiyar garin.

A bangare guda, mayakan Peshmerga 'yan kabilar Kurdawa sun kaddamar da sababbin hare-hare a arewa maso gabashin Mosul inda 'yan kungiyar IS suka yi kaka-gida.

A wani farmakin hadin gwiwa da aka kaddamar a makon jiya, mayakan Peshmerga sun doshi Mosul daga bangaren arewa da gabas yayin da dakarun gwamnati suka tunkare shi daga bangaren kudu.