Za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Somalia

Mutane dubu 14 ne za su kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutane dubu 14 ne za su kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin

Somalia ta shiga wani sabon yanayi mai rikitarwar gaske na shirye-shiryen gudanar da zabe da nufin zabar sabuwar majalisar dokoki.

Masu zabe dubu goma hudu da aka zabo wanda bai ma kai kashi 1 cikin 100 na al'ummar kasar ba sune za su jefa kuri'a wajen zabar 'yan majalisar dokokin 275.

Majalisar dinkin duniya na ganin wannan mataki na samar da wani yanayi da daukacin 'yan Somalia za su samu damar yin zabe daga karshe.

Kazalika majalisar na fatan hakan zai yiwu nan da shekara ta 2020.

Kasar dai ta kwashe shekaru gwammai tana fama da yakin basasa.

Za dai a gudanar da zaben shugaban kasar a karshen watan gobe.