Fursunonin Haiti 170 sun tsere da gidan yarin Arcahaie

Fursunonin sun tsere ne bayan musayar wuta da masu gadinsu
Bayanan hoto,

Fursunonin sun tsere ne bayan musayar wuta da masu gadinsu

Fiye da fursunoni 170 ne suka tsere daga wani gidan yari da ke Arcahaie a Haiti wanda ke da nisan kilomita 45 daga arewacin babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce fursunonin sun yi awon gaba da makamai masu yawa.

An dai kashe wani mai gadin gidan yarin da kuma wani fursuna a yayin da ake musayar wuta.

Tuni mahukunta a kasar suka fara farautar fursunonin inda suke samun taimakon dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da ke kasar.

Gwamnatin kasar dai ta yi alawadai da abin da ya faru a gidan yarin.

Yawancin dai gidajen yarin Haiti akwai cunkoso inda fursunoni kan shafe shekaru ba tare da an yanke musu hukunci ba.