Babu isasshen tsaro a makarantu a Borno —Rahoto

Nigeria schools

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yara a makaranta

Wani sabon bincike ya gano cewa har yanzu babu cikakken tsaro a makarantu a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, fiye da shekaru biyu bayan sace 'yan matan Chibok.

Binciken wanda cibiyar bunkasa rayuwar mata, Women Advocate Research and Documentation Centre, da kuma Gender Equality, Peace and Development Centre suka gudanar, ya nuna babu ingantaccen tsaro na koyon karatu a makarantun gwamnati a jihar.

Rahoton binciken ya ce akasarin makarantun gwamnati a jihar ba sa gudanar da bincike kan baki dake ziyartarsu, kuma basu da isassun masu gadi.

Rahoton ya kara da cewa a akasarin makarantun, akwai cinkoson dalibai, inda a aji guda, akan samu dalibai casa'in.

Binciken ya kuma nuna cewa makarantun da dama ba su da kyakkyawan tsarin sadarwa na gudun-ko-ta-kwana, a inda kuma ake da shi, ba kowane dalibi ba ne ya sanda shi.

Kazalika, binciken ya ce ajujuwa a akasarin makarantun ba su da kofar fitar gaggawa, a inda kuma ake da su, akasarinsu ba su da alama ta nuna amfaninsu.

Hakan a cewa rahoton babban hadari ne na samun turmutsitsi a lokacin fitar gaggawa.

Baya ga sace daliban Chibok, kungiyar ta Boko Haram ta kashe malamai da dalibai da yawa, tare da kona makarantu a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Wani bangare na makarantar sakandiren Chibok da mayakan Boko Haram suka kona

Bayan kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan Chibok a 2014, gwamnatin Najeriya tare da hadin gwiwar kungiyoyin kasa da kasa ta bullo da shirin tabbatar da tsaro a makarantu.

A 2014 ne kuma gwamnatin jihar Borno ta rufe dukkan makarantu a jihar sakamakon hare-haren Boko Haram, lamarin da ya sa daliban Firamare da karamar sakandire zama a gida.

A wasu watanni da suka wuce ne gwamnatin ta sake bude makarantun.