An bukaci shugaba Jocob Zuma yayi murabus

South Africa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaba Jocob Zuma na Afirka ta Kudu

Wani jigo a jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu, yayi kira ga dukkan shugabannin jam'iyyar da su yi murabus, ciki har da shugaban kasar Jocob Zuma.

Mai mukamin mai-tsawatawa na jam'iyar, Jackson Mthembu, ya ce kowa-da-kowa ne yakamata ya dauki alhakin rashin kan-gadon jam'iyyar, wacce ya ce takunta, yafi na gwamnatin nuna wariyar launin fata muni.

Ya kuma bayyana matakin tuhumar ministan kudi na kasar, Pravin Gordhan da aikata cin hanci da rashawa a matsayin bita da kullin siyasa.

Ana dai ci gaba da samun rabuwar kai a jam'iyyar ta ANC, yayin da kuma goyon bayan da take samu ke raguwa saboda zargin cin hanci da ake wa shugaba Zuma, da kuma karuwar rashin aikin yi da sauran matsaloli.