California: Hadarin mota ya kashe mutane 13

Motar kirar bas ta daki bayan wata babbar mota ne

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Motar kirar bas ta daki bayan wata babbar mota ne

Wata motar bas da ke jigilar masu yawon bude idanu ta daki bayan wata babbar mota a kudancin California lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 13 ciki har da direban motar.

Wasu mutanen talatin da daya sun jikkata a hadarin.

Wani likita ya shaidawa manema labarai cewa wasu daga cikin mutanen da hadarin ya rutsa da su sun samu raunuka ne a fuskokinsu saboda rashin daura madaurin kujerar mota wato seatbelt.

Yanzu haka dai 'yan sanda na gudanar da bincike domin gano musabbabin hadarin.