China: An kama masu sayar da gurbatacciyar Madara

An kama wasu mutane 19 a China saboda sake sayar da madarar da ta lalace
Bayanan hoto,

An kama wasu mutane 19 a China saboda sake sayar da madarar da ta lalace

'Yan sanda a China sun kama wasu mutane 19 wadanda ake zargi da sake saka tan din madarar gari fiye da 200 wanda ta lalace a cikin mazubi.

An kama mutanen ne a Shaghai.

Anyi amanna cewa suna kokari ne su su rage asarar da suka yi daga madarar da ba su saida ba wadda aka ajiye har wa'adin shanta ya wuce.

Har yanzu dai ba a samu rahoton ko garin madarar ya yiwa wani illa ba bayan amfani da ita.