Mutanen da 'yan fashin teku suka sako sun isa Kenya

Dan fashin teku

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dukkanin mutanen 26 dai 'yan kasashen Asiya ne

Mutanen nan 26 da 'yan fashin tekun Somaliya suka kwashe kusan shekaru biyar suna garkuwa da su amma suka sako su ranar Assabar sun isa kasar Kenya.

Masu sasantawa sun ce sun kwashe mafi yawancin shekarun tsare a cikin Somaliya.

Mutanen dai sun samu tarbo daga jekadun kasashensu da ke kasar ta Kenya kuma yanzu suna jiran mayar da su kasashen nasu.

'Yan fashin sun kama mutanen ne a cikin wani jirgin ruwan da suke tafiya a ciki daura da gabar ruwan tsibirin Seychelles a watan Maris na shekara ta 2012; daga bisani suka taso keyarsu zuwa Somaliya.