Hadarin Jirgi: Kamaru ta shiga makoki na kasa baki daya

Wurin da jirgi ya yi hadari a Eseka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu dai akwai gawawwakin mutane da yawa da ba a shaida ba.

Shugaba Paul Biya na kamaru ya ayyana zaman makoki na kwana daya ranar Litinin a duk fadin kasar domin juyayin mutuwar 'yan kasar fiye da 70 a cikin wani mummunan hadarin jirgin kasa ranar Jumu'a.

Wannan dai ya biyo bayan kawo karshen aikin ceto masu sauran numfashi daga tarkacen jirgin da kuma zakullo gawawwakin da taragan jirgin suka danne.

Fiye da mutane 600 ne dai suka samu raunuka a hadarin wanda ya faru lokacin da jirgin ya kauce daga kan layinsa a yankin Eseka wanda ke tsakanin manyan biranen kasar biyu - Douala da Yaounde.

Wakilinmu a kasar ta Kamaru ya ce an kiyasta cewa kimanin taragai 11 ne suka jirkice bayan da jirgin ya kauce daga kan layinsa.