Kun san 'yan wasan da ke takarar Ballon d'Or ?

Lionel Messi ne ya lashe gasar a shekarar 2015 a karo na biyar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lionel Messi ne ya lashe gasar a shekarar 2015 a karo na biyar

'Yan wasan Real Madrid Gareth Bale da Cristiano Ronaldo na cikin jerin 'yan wasan da aka fitar da sunayensu domin fafatawar lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya na shekarar 2016, wato Ballon d'Or.

Su ma 'yan wasan Manchester City Sergio Aguero da Kevin de Bruyne na cikin wadanda ke takara, yayin da shi ma dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann ke cikinsu.

Mujallar kwallon kafa ta Faransa na wallafa sunayen 'yan wasa biyar daga cikin 30 da za su fafata don lashe gasar bayan kowacce awa biyu a ranar Litinin.

Fifa dai ta cire hannunta daga bayar da kyautar a watan jiya.

Mujallar kwallon kafa ta Faransa take bayar da kyautar kowacce shekara tun daga shekarar 1956, sai dai shekara shida da suka wuce Fifa ce ke gudanar da gasar.

Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi ne ya lashe gasar a shekarar 2015 a karo na biyar.

Rabon wani dan wasa ban da Messi da Ronaldo ya lashe kyautar tun shekarar 2007, lokacin da dan wasan AC Milan na wancan lokacin Kaka ya lashe.

'Yan wasan Premier biyar - Yaya Toure, Aguero, De Bruyne, Alexis Sanchez da kuma Eden Hazard - na cikin jerin wadanda suka fafata domin lashe gasar a bara, sai dai Bale ne kadai dan wasan Birtaniya da ke jerin a bana.

'Yan wasan da aka fitar kawo yanzu da ke takarar Ballon d'Or a 2016'

Sergio Aguero (Manchester City), Pierre-Emerick Aubameyang (Borussia Dortmund), Gareth Bale (Real Madrid), Gianluigi Buffon (Juventus), Cristiano Ronaldo (Real Madrid), Kevin de Bruyne (Manchester City), Paulo Dybala (Juventus), Diego Godin (Atletico Madrid), Antoine Griezmann (Atletico Madrid), Gonzalo Higuain (Juventus).