Adam A. Zango ya dakatar da yin fim

Zango ya ce ya fi masu digiri

Asalin hoton, Adam zango

Fitaccen jarumin nan na fina-finan Kannywood, Adam A. Zango, ya ce daga yanzu ba zai ci gaba da fitowa a fina-finai ba.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na , Zango ya ce "zan yi amfani da wannan damar don bai wa masoya kallon fina finaina... hakuri a kan na dakatar da yin fim".

Ya kara da cewa "zan tsaya iya waka domin na samu sauki da kwanciyar hankali".

A ranar Lahadi ne muka wallafa labarin da ke cewa jarumin ya yi tsokaci kan masu shaidar karatun digiri.

Sai dai Adam Zango ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi, inda ya ce "ina bai wa 'yan boko hakuri a kan abin da @bbchausa suka ce na fada game da masu degree. A gafarce ni".

Jarumin ya kuma goge sakon da ya wallafa din wanda akansa ne muka gina labarin.

'Sakon da ya fara wallafawa'

Zango ya ce BBC ce ta hana shi yin fim

Asalin hoton, Adam a zango

Bayanan hoto,

Kalaman da Adam A. Zango ya wallafa a harshen Turancin Ingilishi

A sakon da ya fara wallafawa a shafinsa na Instagram, wanda tuntuni ya goge, jarumin ya yi shagube cewa shi ba shi da shaidar kammala karatu ta digiri amma ya fi masu digiri amfani.

A cewarsa, "Idan ka mallaki digiri baka da aiki. Ni kuwa ba ni da digiri amma shekara 12 ina da aikin yi. Ko da kana da aiki idan na rera waka daya zan samu kudin da suka fi albashinka."

Da alama dai yana yin raddi ga wasu ne, wadanda bai fadi sunan su ba.

Zango ya ce bai iya turancin ba, yana mai cewa wadanda suka iya turancin sai su "ci shi" idan abinci ne, yayin da shi kuma zai rika yin larabci.

Sai dai wannan batu ya jawo masa suka daga wajen wasu masu amfani da shafukan sada zumunta, inda daya daga cikinsu ke cewa "ai ni ban taba jin Zango ya yi larabci ba."