Ya kamata Buhari ya yi adalci - Gwamnonin APC

Asalin hoton, Getty Images
An zargi gwamnatin Shugaba Buhari da yin tafiyar hawainiya
Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulkin Nigeria sun nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi adalci da daidaito wurin nada jakadun kasashen waje.
A ranar Alhamis ne shugaban ya mika sunayen mutum 46 zuwa ga majalisar dattawan kasar domin ta tantance su don zama jakadun kasar a kasashen waje.
Sai dai batun ya tayar da hargitsi a fagen siyasar kasar, inda wasu da dama suke korafin cewa ba a zabo wadanda suka yi wa jam'iyyar hidima ba.
Gwamnonin sun mika koken su ne a rubuce bayan wata ganawa da suka yi da shugaban a fadarsa a ranar Litini.
Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau ya shaida wa manema labarai cewa Shugaba Buhari ya yi alkawarin duba korafe-korafen da jihohin suka gabatar.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da uwargidan shugaban, Aisha Buhari, ta shaida wa BBC cewa mijin na ta yayi watsi da mafi yawan mutanen da suka tallafa masa a yakin neman zabe.
Wasu daga cikin mutanen da shugaban kasa ya nada sun hada da Usman Bugaje, Yusuf Tugar, Musa Ibeto, Jamila Ahmadu-Suka, Sanata Olorunimbe Mamora, Nurudeen Mohammed, Suleiman Hassan da Pauline Talen.
Sai dai tuni wasu daga cikin wadanda aka nada din, kamar tsohuwar mataimakin gwamnan Plateau, Pauline Tallen, suka yi watsi da nadin na su.
Rahotanni sun ce akwai yiwuwar shugaban zai sauya wasu daga cikin sunayen, domin ita kanta uwar jam'iyyar APC ta kasa ba ta gamsu da wasu daga cikinsu ba.