Nigeria: Avengers ta fasa bututun mai a Naija Delta

Niger Delta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hare-haren na janyo wa Nigeria asarar kudaden shiga

Masu tayar da kayar baya na kungiyar Niger Delta Avengers sun yi ikirarin kai hari kan wani bututun mai mallakar kamfanin Chevron a Kudancin kasar.

Harin na zuwa ne 'yan kwanaki kalilan kafin sanar da ranar gudanar da tattaunawa tsakanin masu fafutukar da kuma gwamnati, domin kawo karshen hare-haren da ake fama da su.

A sakon da ta wallafa a shafinta na intanet, kungiyar ta kuma gargadi kamfanonin kasa-da-kasa da kada su kuskaru su gyara duk wani bututun mai da suka lalata.

Kawo yanzu kamfanin Chevron ya ki ya tabbatar da ko an kai harin ko kuma a'a.

Haka kuma ya ki ya yi wani karin bayani a game da lamarin.

Kafin soma kai hare-hare a farkon bana, kasar na hako gangar danyen mai sama da miliyan biyu a kullum, kafin harin ya sa ya koma ganga miliyan daya da kadan.

Hakan da kuma faduwar darajar man a duniya, sun kara jefa tattalin arzikin Najeriyar, wadda ke fama da karancin kudaden shiga, cikin rudani.

Masu fafutukar sun ce suna takaddamar ne domin ganin al'ummominsu sun samu babban kaso na arzikin man da ake hakowa a yankin na su.