Nigeria: Patience Jonathan ta kai karar EFCC

Goodluck Jonathan da Patience Jonathan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Patience Jonathan ta musanta aikata kowanne irin laifi

Uwargidan tsohon shugaban Nigeria Goodluck Jonathan, ta kai karar hukumar yaki da cin hanci ta EFCC kan wasu asusunta na banki da hukumar ta dakatar.

Patience Jonathan, ta nemi kotu ta sa EFCCn ta biya ta diyyar dala miliyan 200, saboda a cewarta, an take mata hakkinta.

Kazalika ta kuma nemi kotun da ta tilasta wa hukumar bude mata asusun nata na Skye Bank, wadanda aka rufe a watan Yuli.

Kimanin mata 100 ne suka yi zanga-zanga a gaban kotun a birnin Legas, domin nuna goyon baya ga Mrs Jonathan.

Hukumar EFCC ta dakatar da asusun ne, saboda tana zarginta da halatta kudaden haram.

Adadin kudaden da aka ce an rufe a asusun Misis Jonathan sun kai dala miliyan 15.

Sai dai Patience Jonathan ta musanta aikata kowanne irin laifi.

Alkalin kotun ya sanya ranar 7 ga watan Disamba, domin cigaba da sauraron shari'ar.

Tsoffin jami'an gwamnatin mijinta da dama ne ke fuskantar shari'a da kuma bincike kan zargin cin hanci da rashawa, tun bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari.

Shi kansa Mista Jonathan ya ce gwamnatin Buhari na bincikarsa kan zargin cin hanci da rashawa.