An fasa tuhumar ministan kudin Afirka ta Kudu

Ministan Kudin kasar Pravin Gordhan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pravin Gordhan (na tsakiya) ya samu yabo saboda yadda yake son a takaita kashe kudaden gwamnati

Ofishin babban mai gabatar da kara a Afirka ta Kudu ya janye tuhumar da yake yi wa Ministan Kudin kasar Pravin Gordhan.

Mista Gordhan ya bayyana tuhumar da cewa ba ta da tushe, kuma siyasa ce kawai.

Labarin tuhumar da aka bayyana a farkon watan nan ta razana kasuwannin kudade sannan darajar kudin kasar ta fadi da kashi uku cikin dari.

A bara ne aka nada ministan kudin bayan da mutumin da Shugaba Jacob Zuma ya fi so, ya bar mukamin bayan 'yan kwanaki kacal.

Shi dai ba ya daga cikin mafiya kusanci da shugaban, kuma ya yi gargadin cewa cin hanci na kara zama ruwan-dare a kasar.

Tuhumar na da alaka da wasu kudaden alawus da aka biya wasu manyan jami'an hukumar haraji ta kasar, lokacin tana karkashin jagorancin Mista Gordhan shekara 10 da ta wuce.