Pauline Tallen ta bayar da uzurin kin karbar jakadanci

Bayanan sauti

Uzurin Pauline Tallen

A Najeriya, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Filato Pauline Tallen ta ce ba za ta karbi mukamin jakadanci da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada ta ba.

Misis Tallen na daya daga cikin mutane 46 da shugaban ke niyyar nadawa jakadun Najeriya a kasashen waje.

A wata hira da ta yi da BBC, ta ce tsananin rashin lafiyar mai-gidanta da kuma tsarin rabon mukamai a jiharsu ta Filato su ne dalilanta na kin amince wa da mukamin na jadakiya.

Batun nada jakadun dai na haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki.

Su ma gwamnonin jam'iyyar ta APC sun yi korafi ga shugaban kan yadda ya zabo mutanen da ya ke so ya nada.

A makon jiya ne dai shugaban ya mika sunayen mutane 46 ga Majalisar Dattawan kasar, wadanda ya ke son nadawa jakadu, domin majalisar ta tantance su.