Jami'ai a Kamaru na neman tallafin jini daga al'ummar kasar

Jirgin da yayi hadari a Kamaru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Har yanzu dai dangogin wadanda suka rasu suna kokarin gano gawarwakinsu

Jami'ai a Kamaru sun yi kira ga jama'a da su bada gudummuwar jini domin taimakawa wajen kula da mutane 600 da suka jikata a hadarin jirgin kasa da ya abku a kasar.

A ranar Lahadi ne dai aka gano karin gawarwaki 11 wanda hakan yasa yawan mutanen da suka mutu ya kai 80.

Jakadar Faransa da ke kasar na daga cikin fitattun mutanen da suka bada gudummuwar jini inda kuma ya bukaci sauran al'umma da su bi sahu.

Hadarin dai ya abku ne lokacin da jirgin ya kauce daga kan layinsa a yankin Eseka wanda ke tsakanin manyan biranen kasar biyu - wato Douala da Yaounde.

Shugaba Paul Biya ya sanar a gidan talabijin na kasar cewar gwamnati zata dauki nauyin kula da mutanen da suka jikkata a hadarin.

A ranar Litinin ne dai aka ayyana zaman makoki na kwana guda a duk fadin kasar domin juyayin mutuwar fiye da mutane 70 a mummunan hadarin jirgin kasa daya abku ranar Jumu'ar data gabata.