Faransa: An kwashe 'yan gudun hijira 1600 daga sansanin Calais

Sansanin 'yan gudun hijirar Jungle da ke Calais a Faransa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun shaida wa BBC cewa ba za su bar Sansanin ba

An kwashe kusan mutum 1,600 a motoci daga sansanin 'yan gudun hijira na Calais ko kuma "Jungle" a kasar Faransa, a wani bangare na shirin kwashe mutanen gaba daya.

Akalla mutam 7,000 ne suke rayuwa cikin mummunan yanayi a sansanin.

Motoci 40 cikin 60 wadanda za su debe mutanen sun kwashe wasu 'yan gudun hijarar sun tafi da su wasu cibiyoyi a cikin kasar ta Faransa.

Ana fargabar wasu ba za su yarda su tafi ba saboda suna so su shiga Ingila, kuma akwai yiwuwar kara aukuwar tarzomar da ta faru tsakaninsu da 'yan sanda a karshen makon da ya gabata.

A ranar Talata ne dai ake sa ran za a fara rusa sansanin.

A ranar Litini ne Birtaniya ta dakatar da karbar wasu daga cikin yara 'yan gudun hijira 1,300 da aka yi kiyasin ba sa tare da iyayensu bayan da Faransa ta nemi da ta yi hakan.

Wasu masu aikin sa-kai sun yi korafin cewa ba a bai wa 'yan gudun hijirar cikakkaen bayani ba a kan abin da aka tsara gudanarwa a ranar, kuma hakan ya jawo rudani da cunkoso.