An samu karuwar mata masu shana barasa

Nau'o'in barasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Binciken yabada shawarar ya kamata jami'an lafiya su maida hankali akan mata

Wani bincike da aka gudanar, ya gano cewa adadin mata masu dabi'ar shan barasa ya kusan kamo na yawan mazan da ke shan ta idan aka kwatanta da adadin barasar da suke sha.

Wani bincike da aka yi kan mutanen da aka haife su tsakanin shekarun 1991 da 2001 ya nuna yawan matan da ke shan barasa ya karu.

Kuma an danganta hakan da dalilai masu yawa ciki har da raguwar farashin barasa da kuma ci gaban da kamfanonin yin ta suka samu.

A karshe masu binciken na jami'ar New South Wales a Australia sun bada shawarar ya kamata hukumomin lafiya su maida hankali kan mata.

Wannan lamari dai ya fi kamari ne a kasashen yankin Amurka da kuma Australia.

Akwai dai mashaya giya da dama a nahiyar Afirka.