Faransa: Za a fara rushe matsugunin 'yan cirani

'Yan cirani a sansanin Calais

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro masu kula da kwashe 'yan ciranin Calais, na fatan kammala aikin nan da gobe laraba.

Nan gaba kadan ne ake sa ran za a fara aikin rushe sansanin 'yan cirani da ke garin Calais a arewacin kasar Faransa wanda aka fi sani da Jungle.

A jiya litinin ne aka kwashe kusan kashi daya cikin 'yan cirani 8000 da ke zaune a sansanin, inda aka rarraba su wurare daban-daban a kasar Faransar.

Wakilin BBC ya ce ana saran za a sake kwashe wasu a yau talata, kuma za a fara aikin rusau din a yau talata, wannan dai alama ce da ke nuna an dauki koken da mutanen Calais suka yi na zaman yan ciranin a wurin da matukar muhimmanci.

Ya yin da ga hukumomi suka ce za a sanya ido sosai a dan tsakanin nan, dan gujewa sake zaman wasu sabbin 'yan ciranin a wurin, wanda hakan na nufin daukar matakan tsaro baya ga matakin rushe shi.