Nigeria: Buhari na kokarin dinke rikicin APC

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A baya dai shugaba Muhammadu Buhari ya ki cewa uffan kan batun rikicin na APC.

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya fara mika-wuya ga matsin-lambar da wasu `yan kasar ke yi cewa ya kamata ya sa baki wajen magance rikice-rikicen da ke damun jam`iyyar su ta APC.

Mutane da dama ciki har da matarsa na korafin cewa ba a damawa da wadanda suka yi wa jam`iyyar dawainiya wajen nadin mukamai.

Kawo yanzu dai shugaban kasar ya gana da gwamnonin jam`iyyar, haka kuma ya fara daukan matakan sasantawa da wasu jiga-jigan jam`iyyar, wadanda ake zargin cewa sun fara juya wa jam`iyyar baya.

Wasu dai sun bada shawara idan za a bada muhakamai na siyasa, a tabbatar an raba tsakanin dukkan bangarori, dan kowa magance korafin cewa ana nuna fifiko.

Jam'iyyar APC dai na fama da rikicin cikin gida, musamman a rassan jam'iyyar da ke jihohin kasar.

Lamarin da wasu ke ganin cewa matukar ba a shawo kan matsalar ba da dinke barakar da ke tsakanin su akwai jan aiki a gaban jam'iyyar nan gaba.

A baya dai masana sun yi ta kira ga shugaban kasar da ya yi amfani da matsayinsa wajen kashe wutar rikicin jam`iyyar, amma mukarrabansa na cewa ba ya shisshigi.