Mata 'yan majalisa na fuskartar cin zarafi

Asalin hoton, Getty Images
Matan na fuskantar barazana ko dai ta cin zarafi ta hanyar lalata da su, ko ta hanyar dukan su
Wani rahoton hukumar da ke sa ido kan harkokin majalisu ta duniya wato International Parliamentary Union ta fitar, ya nuna cewa an samu karuwa a barazanar da mata 'yan majalisun ke fuskanta na yin lalata da su.
IPU ta kafa wannan hujjar ne bayan tattaunawa da mata 'yan majalisu 50 daga kasashen Afurka da Asiya, da Turai, da Amurka da kuma kasashen Larabawa.
Kusan kashi tamanin cikin dari sun ce yawancin sun fuskanci cin zarafi ko dai ta hanyar lalata da su, ko kuma dukan su.
Tsohuwar Firaiministar New Zealand Helen Clark, kuma jami'a a hukumar ayyukan MDD ta ce akwai jan aiki a gaba dan shawo kan matsalar.
Ta ce a yawancin Majalisun mata na ganin dabi'un maza a kan su tamkar barazana ko kuma tsokanar fada, ana yawan yunkurin cin zarafin su, dan haka akwai jan aiki a gaba dan shawo kan matsalar.
Shi ma sakatare Janar na hukumar IPU Martin Chungong ya shaidawa BBC cewa barazar da mata 'yan majalisun ke fuskanta na hana su gudanar da ayyukan su a majalisa.