Trump: Hillary za ta janyo yakin duniya na uku

Mista Trump da Misis Clinton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mista Trump ya ce idan ta dauki matakin tursasa Assad ya sauka daga mulki, to za a afka yakin duniya na uku

Dan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump, ya ce matakan da abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar Democrat Hillary Clinton ta ce za ta dauka a kasar Syria na matsawa shugaba Basharul Assad lambar ya sauka daga mukamin sa, babu abinda zai haifar fa ce haddasa yakin duniya na 3.

Mista Trump ya ce kamata ya yi mu maida hankali wajen murkushe kungiyar IS mai ikirarin jihadi, bai kamata mu maida hankali kan Syria ba, idan aka bi tsarin da ta ke son amfani da shi, to tabbas za mu kare da yakin duniya na 3

Misis Clinton dai ta nanata cewa idan ta zama shugabar kasar, za ta kebe wani yanki a Syria da jiragen sama ba za su bi ta wurin ba, inda ta ce hakan zai taimaka wajen tserar da dinbin fararen hular da ke mutuwa, kuma zai kawo karshen yakin da ake yi a kasar cikin gaggawa.

Sai dai masu sukar ta na cewa wannan mataki zai janyo, a fada yaki da jiragen sama marasa matuka na kasar Rasha.