Clinton na so a soma yakin duniya na uku - Trump

Trump ya soki 'yan Republican

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Trump ya soki 'yan Republican

Dan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump ya ce tsare-tsaren abokiyar hamayyarsa ta Democrat kan kasar Syria za su kai duniya ga faraa yakin duniya na uku.

Trump ya ce ya kamata Amurka ta mayar da hankali wajen kawar da kungiyar IS maimakon kan yadda za ta cire shugaban Syria daga kan mulki.

Mrs Clinton dai ta idan ta zama shugabar kasar, za ta kebe wani yanki a Syria da jiragen sama ba za su rika wucewa ta kansa ba, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen tserar da fararen hular da ke mutuwa, kana ya kawo karshen yakin da ake yi a kasar cikin gaggawa.

Sai dai wasu manyan jami'an rundunar sojin Amurka sun ce matakin zai janyo a fada yaki da jiragen sama kasar Rasha da ke yankin.

Ofishin yakin neman zaben Mrs Clinton ya zargi Mr Trump da "tsorata Amurkawa."

Kazalika Mr Trump ya caccaki 'yan jam'iyyarsa ta Republican saboda kin goyon bayan takararsa.

Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a Florida cewa "Da a ce mun hada kawunanmu ba zai yiwu mu sha kaye a hannun Hillary Clinton a wannan zaben ba."