Ina cikin bala'i a Manchester —Mourinho

Manchester United ta sha kashi a wasanni uku cikin tara na farko da suka buga a gasar lig tunda Mourinho ya zama koci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United ta sha kashi a wasanni uku cikin tara na farko da suka buga a gasar lig tunda Mourinho ya zama koci

Jose Mourinho ya ce zaman da yake yi shi kadai a Manchester ya zame masa "wani bala'i", yana mai cewa ya gaji da ganin masu daukar hoton da suka yi dandazo a wajen otal din da yake zama.

Mourinho, mai shekara 53, na zaune ne a otal din Lowry tun lokacin da aka nada shi a matsayin kocin United a farkon kakar wasa ta bana.

Ya kara da cewa ya tsani ya rika fita waje saboda yawan 'yan jaridar da ke damunsa.

Kocin na United ya shaida wa Sky Sports cewa, "Ina son fita waje na tsallaka gada domin zuwa wajen sayar da abinci, amma ba zan iya ba [saboda masu daukar hoto]. Lamarin na da ban haushi."

United dai ba su taka rawar gani ba tunda Mourinho ya karbi ragamar tafiyar da kungiyar.