Rooney yana da matukar muhimmanci— Southgate

Rooney (wanda ke baya daga gefen hagu) ya shiga wasan da Ingila da Slovenia suka tashi 0-0 a minti 73 da wasan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rooney (wanda ke baya daga gefen hagu) ya shiga wasan da Ingila da Slovenia suka tashi 0-0 a minti 73 da wasan

Kocin riko na Ingila Gareth Southgate ya ce har yanzu kyaftin din tawagar kwallon kafar kasar Wayne Rooney yana da "matukar tasiri", duk da cewa ba ya haskakawa a Manchester United.

Ba a sanya Rooney, mai shekara 31, a wasan da Chelsea ta doke United 4-0 ba ranar Lahadi saboda ya ji rauni.

Haka kuma ba a sanya shi a wasanni uku na Premier da kungiyar ta buga ba sai a matsayin wanda zai maye gurbin wani dan wasan, kuma sau daya kacal ya zura kwallo a kakar wasa ta bana.

Southgate, wanda bai sanya Rooney a wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya da tawagar Ingila ta yi da Slovenia a wannan watan ba, ya ce shugabancinsa na da matukar ban sha'awa.

Southgate ya kara da cewa: "Rooney shi ne kyaftin din Ingila, kuma kodayake bai shiga wasan da muka yi da Slovenia ba, a wurina shi dan wasa ne mai matukar muhimmanci kamar yadda kowa ma ya sani."