Sasha ta zolayi mahaifinta Barack Obama

Sasha Obama ta aika da sakon Snapchat inda ta nuna cewa rayuwa ta gundire ta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sasha ta aika da sakon Snapchat inda ta nuna cewa rayuwa ta gundire ta

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewa karamar 'yarsa, Sasha, ta zolaye shi a shafin aikewa da sakonni na Snapchat.

Shugaban ya yi wannan bayani ne a shirin talabijin na Jimmy Kimmel ranar Litinin.

Obama ya ce Sasha ta nadi maganganunsa lokacin yana tattaunawa kan shafukan sada zumunta a wurin da shi da sauran iyalinsa ke cin abincin dare, sannan ta aikawa kawayenta.

Ba wannan ne karon farko da shugaban kasar ta Amurka ke yin bayani kan yadda 'yar tasa mai shekara 15 take amfani da shafukan sada zumunta ba.

A watan Yuli, Shugaba Obama ya ce Sasha ta aika da sakon Twitter, lamarin da ya sa gidajen watsa labarai suka yi ta yin ruguguwar neman shafinta na Twitter, sai dai har yanzu basu sani ba.

Kazalika, ba a bayyana sakon Snapchat din da ta aikawa kawayen nata ba.

An tsara sakonnin Snapchat ne ta yadda za su rika bacewa bayan wani dan lokaci, kodayake akwai hanyoyin da za a hana su bacewar.