Hukumar FA ta tuhumi Jose Mourinho

Mourinho ya ce ya zaman da yake yi shi kadai a Manchester bala'i ne

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mourinho ya ce zaman da yake yi shi kadai a Manchester bala'i ne

Hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA), ta tuhimi kocin Manchester United Jose Mourinho kan ikirarin da ya yi cewa abu ne mai wahala ga alkalin wasa Anthony Taylor ya iya hura wasan da United ta yi da Liverpool.

Mourinho ya kara da cewa nada Taylor domin ya yi alkalancin wasan da suka yi ranar 17 ga watan Oktoba ya matsa masa lamba.

Dokar kwallon kafa dai ta hana koci ya yi tsokaci kan alkalin wasa gabanin a yi wasan.

Yanzu dai an bai wa Mourinho wa'adin ranar 31 ga watan Oktoba domin ya yi bayani kan wannan hali mara kyau da ya nuna, lamarin da ya kaskantar da wasan kwallo.

Taylor ya bai wa 'yan wasa ruwan-dorawar kati sau hudu a wasan da suka tashi 0-0.