Kamfanonin man Nigeria sun kori ma'aikata 3,000

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatan sun bukaci gwamnati ta dauki mataki
Kungiyar kwadago ta Najeriya ta ce kamfanonin hakar man fetur na kasashen waje a kasar sun kori akalla ma'aikata 3,000.
Shugaban kungiyar ma'aikatan man fetur, Igwe Achese, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya kamata gwamnatin Najeriya ta kalubalanci matakin.
A cewarsa, "Ya kamata gwamnati ta taka birki ga matakin da kamfanonin mai na kasashen waje ke dauka. Sai korar mutane kawai suke yi suna rufe kamfanoninsu."
Mr Igwe Achese ya kara da cewa ma'aikatan sun bai wa kamfanonin wa'adin kwana 21 domin su daina korar ma'aikatan da suke yi, yana mai cewa idan sun ki ji ba sa ki gani ba.
Jaridar Premium Times, wacce ake wallafawa a shafin intanet, ta ce Exxon Mobil, Chevron, Pan Ocean da kuma Saipem na cikin kamfanonin man da suka kori ma'aikata.
Sai dai duka kamfanonin ba su ce komai ba game da zargin korar ma'aikatan.