Sojoji sun kashe mayakan IS '900' a Iraqi

Sojojin Iraqi na ci gaba da dannawa zuwa Mosul

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sojojin Iraqi na ci gaba da dannawa zuwa Mosul

Wani Janar na sojin Amurka ya ce an kashe 'yan kungiyar IS tsakanin 800 zuwa 900 tun lokacin da dakarun Iraqi suka kaddamar da hare-hare domin kwato birnin Mosul a makon jiya.

Joseph Votel ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP zai yi wahala a san hakikanin adadin mayakan IS din da aka kashe saboda suna sajewa da fararen-hula.

An yi ittifakin cewa kawai mayakan IS 5,000 a birnin na Mosul tun da aka fara kai musu farmaki.

Tun daga lokacin, dakarun sojin Iraqi da na masu fafutika, tare da tallafin sojojin Amurka sun kwace garuruwa da dama daga hannun IS.

Manyan jami'an rundunar sojin kasar sun yi gargadin cewa za a kwashe makonni ko ma watanni da dama kafin a iya kwace birnin.