An amince da dokar da za ta kori shugaban Ghana

Fadar shugaban kasar Ghana

Asalin hoton, GHANA PRESIDENCY

Bayanan hoto,

Fadar shugaban kasar Ghana

Majalisar dokokin Ghana ta amince da wani kudirin doka da zai sa a kori duk wanda ya zaman shugaban kasar da karfin tsiya idan bai fita daga gidan gwamnati a kan lokaci bayan wa'adinsa ya kare ba.

Kudirin dokar ya ce dole ne shugaban kasar da mataimakinsa su fita daga gidan gwamnati, sannan su mika motocin da ake tuka su akalla mako biyu kafin a rantsar da duk wanda ya zama shugaban kasar.

Kazalika kudirin dokar ya ce su ma ministoci za su mika kayan gwamnati akalla wata guda kafin a rantsar da sabuwar gwamnati.

An yi dokar ne domin a rage jan-kafar da shugabanni ke yi na mika kayan gwamnati a kan lokaci a yayin da ake shirin yin zaben shugaban ranar bakwai ga watan Disamba.

Yanzu dai ana jiran shugaban kasa ya sanya wa kudirin dokar hannu domin ya zama doka.