Ana tuhumar 'yan takarar Ghana biyu da rashawa

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Ghana na shirin zaben shugaban kasa ranar 7 ga watan Disamba
Wa'adin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Ghana EOCO ta bai wa wasu 'yan takarar shugabancin kasar biyu da aka hana shiga zaben na bayyana hanyoyin samun kudaden kamfe dinsu ya cika.
Hukumar ta bai wa mutanen biyu har zuwa ranar Laraba domin fayyace yadda suka samu kudaden da suke kashewa a zaben da za'a gudanar a watan Disamba.
Hukumar ta bukaci 'yan takarar su bayyana a gabanta ne domin amsa wasu tambayoyi.
Dr Paa Kwesi Nduom na jam'iyyar PPP na daya daga cikin 'yan takarar da hukumar ke nema, kuma yace ba zai amsa kiranta ba, tunda ba ta gayyace shi a hukumance ba, sai jita-jita da yake ji kamar kowa a gari, cewa tana neman sa.
Ita kuwa jam'iyyar APC ta Mallam Hassan Ayariga ta ce bita da kulli ake yi wa dan takararta, don ganin cewa ba ayi zaben shugaban kasar da shi ba.
Hakan na zuwa ne a yayin da wasu daga cikin 'yan takarar zaben shugaban kasar suka shigar da kara kotu domin kalubalantar soke su daga shiga takarar da hukumar EOCO ta yi.
Ghana na shirin gudanar da zaben shugaban kasar ne ranar 7 ga watan Disamba 2016.