Ikechukwu Ike ya ce ya ga alfanun sana'ar aski

Bayanan sauti

Mai askin baba a Najeriya

A Najeriya, yayin da gwamnati ke kokarin yaki da cin hanci da rashawa, akwai dubban matasa a sassan kasar da suka dukufa wajen neman na kansu.

Matasan sun dauki hanyar cimma burin nasu cikin hakuri da wadatar zuci, inda suke tafiyar da rayuwarsu da samun abin biyan bukatun yau da kullum.

Ikechukwu Ike, wani mazaunin jihar Enugu ne da ke kudu maso gabashin Najeriya, wanda ya ce ya fara sana'ar askin baban tun da ya kammala makarantar sakandire shekaru ashirin da suka gabata.

Mista Ike ya kuma ce ya dauki shawarar yin hakan ne bayan da ya lura cewa ba zai samu shiga jami'a ba. Daga nan, a cewarsa sai ya dukufa ya koyi yadda ake askin baba ko kuma kwas-kwas.

Wannan sana'ar tasa har ta kai shi ga cimma wasu nasarori, musamman wajen biyan bukatunsa na yau da kullum.

Zaku iya sauraron hirarsa da wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed a farkon wannan rahoto.

Bayanan hoto,

Sana'ar Ikechukwu Ike, tasa har sun kai shi ga cimma wasu nasarori, musamman wajen biyan bukatunsa na yau da kullum