Girgizar kasa ta daidaita wasu sassan kasar Italiya

Yadda girgizar kasar ta lalata gine-gine.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ko a watan Agusta sai da girgizar kasa ta hallaka sama da mutane 300 a kasar Italiya

Hukumar agajin gaggawa ta kasar Italiya ta shafe tsahon dare ta na aiki tukuru, bayan karfafan girgizar kasa sun afkawa tsakiyar kasar na tsahon sa'a biyu.

Lamarin ya faru ne a kusa da yankin da irin wannan girgizar kasa ta hallaka mutane kusan dari uku a watan Agusta da ya wuce, a birnin Perugia.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane su ji mummunan rauni, sai dai rashin kyawun yanayi ya sanya ba za a iya isa sauran wurare dan gano irin barnar da girgizar kasar ta haddasa.

Shugabannin yankin sun bayyana cewa an samu katsewar wutar lantarki, gine-gine sun ruguje, ya yin da lamarin ya munana a kauyuka.

Yawancin mutane dai sun yi kokarin ficewa daga muhallansu a lokacin da girgiza ta farko ta afku, hakan kuma zai taimaka wajen rage yawan wadanda lamarin zai rutsa da su.