Ana ci gaba da kin tayin aiki da gwamnatin Buhari

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masana na ganin cewa kara mutanen suka yi na kin bayyana dalilan su an kin karbar mukaman

Masana a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakin su game da maida hannun kyauta baya da wasu wadanda shugaba Muhammadu Buhari ya gayyata dan su yi aiki tare suka yi.

Wannan dai a iya cewa wani sabon lamari ne mai daure-kai, saboda ba kasafai ake ganin hakan ta faru ba.

Cikin wadanda suka juya wa tayin baya, har da wadanda aka yi niyyar nada musu mukamin jakadu da kuma shugabancin wasu hukumomi.

Wasu daga ciki dai sun gabatar da hanzarin cewa ba za su samu sukunin aiki da gwamnatin ba, sakamakon hidimomin da ke gabansu, amma masana sun ce akwai wasu dalilai na daban.

A dan tsakanin nan kusan mutane uku ne suka yi godiya da tayin da shugaba Buharin ya musu, ciki kuwa har da Dakta Usman Bugaje.

Masana kimiyyar siyasa a Najeriyar irin su Dakta Abubakar Kari na ganin cewa kara ko kawaici wadannan mutane ke yi, dan haka ba su fito fili sun bayyana dalilin su na kin karbar ta yin ba ya yin da wasu tun fil azal ma ba a tuntube su ba kan batun.